9 Satumba 2020 - 10:47
COVID-19:Jami’ar Oxford Ta Dakatarda Gwajin Alluran Riga Kafin Cutar Korona

Jami’ar Oxford ta kasar Burtaniya ta dakatar da gwaji alluran riga kafin cutar Corona bayan da ta gano cewa allurer ta bayyana wata illarta a jikin wani da ta yi wa gwaji.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya bayyana cewa jami’ar ta dauki wannan matakin ne a karon farko bayan da ta gano cewa alluran ta samar da illa ga wani wanda aka yi wa gwajin alluran a kasar ta Burtania.

Duk da cewa jami’ar ba ta bayya irin illar da alluran ta haddasa ga wanda ta yi wa gwajin ba, amma wannan ya farkar da mutane kan yin taka tsantsan da alluran riga kafi wadanda ake tsere wajen samar da su a duniya.

Jami’ar Oxford dai ta na daga cikin cibiyoyin da suke aikin samar da alluran riga kafin cutar korona kimani 150 a duniya. Sannan ana saran kafin karshen wannan shekara akalla guda 6 daga cikinsu zasu kammala aikin gwaje-gwajinsu.

Tuni dai gwamnatin kasar Britania ta sayi alluran riga kafin na jami’ar Oxford guda miliyin 100.

342/